Daliban Jami'a Sun Yi Zanga Zanga

Daliban jami’ar jihar Kogi a yau alhamis sun yi zanga zangar nuna damuwarsu akan yajin aikin da Malaman makaranta keyi, wanda a yanzu ya kai har watani ukku.

Wannan zanga zangar dai ta jawo cikas ga zirga zirgar motoci akan hanyar Lokoja, wanda ya jefa matafiya cikin mawuyacin hali, kasancewar hanyar mahadar arewa da kudancin Najeriya.

Su dai, malaman suna yajin aikin ne saboda rashin biyan su albashi, abinda jami’an gwamnatin jihar suka ce bashi ne da malaman ke bi tun lokacin gwamnatin Idri Wada.

Shugaban kungiyar malaman makarantan Daniel Aina, yace zasu ci gaba da yajin aikin sai an biya su kudaden da suke bin gwmanati.