Yawan Fyade Yana Karuwa

'Yan mata

A yau ne hukumar dake kula da kyautata rayuwar mata da yara da al'umma ta Damagaram ta gudanar da wani bita na wayar da kai akan makomar ‘yan mata. An yi shugulgula a karkashin jagorancin gwamnan jihar Damagaram, maudu'in ranar shi ne saka jari don kyautata tarbiyar ‘yan mata.

A cewar shugaban ma’aikatar dake kula da kyautata rayuwar mata da yara kanana a Damagaram, madam Rabi, wannan kudiri na kyautata makomar ‘yan matan bai zo kai tsaye ba idan aka dubi irin matsalolin da ‘yan matan ke cin karo dasu masamman a Damagarm, kamar auren dole rashin ilimi musgunawa da sauransu.

Idan kuma aka yI la’akari da yawan ‘yan matan sun kai kimanin miliyan ukku a kasar ta Nijar, kuma sunanan kara zube, saka jari a harkar ‘yan matan na nufin kawo dauki ga tarbiyarsu lafiya da kariyarsu.

Abdulrahman Liman mai kula da wannan sashen a hukumar dake kula da al’uma a jihar Damagaram, yace wannan shine kulawa da matasa ‘yan mata, domin idan har mace ta sami ilimi to al’uma ta rayu idan kuma aka sami akasin haka toh al’uma ta shiga wani hali.

Shi kuwa gwamnan jihar Damagaram, malam Isa Musa, kira yayi ga iyaye dasu maida hankali wajen tarbiyar ‘ya’yansu.

Hajiya Ummadeen shugabar kungiyar dake yaki da musgunawa mata, tace abinda mata suka fi cin karo dashi shine fyade, domin a cewar ta rahotanin fyaden da suka samu a wannan shekarar yafi na bara.

Your browser doesn’t support HTML5

Yawan Fyade Yana Kara Karuwa - 3'45"