Portugal Ta Sami Galaba Kan Faransa A Wasan Karshe Na Cin Kofin Euro 2016

Kungiyar kwallon kafa ta Portugal ta lashe kofin Euro 2016 a sakamakon jefa kwallo guda bayan Karin lokacin da aka yi masu duk kuwa da raunin da shahararren dan wasannan Cristiano Ronaldo ya samu kafin hutun rabin lokaci.

Tsohon dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Swanse Eder ya canji Renato Sanches, wanda a kusan karshen rabin laokaci ne ya murda kwallon daga gefe guda dab da mai tsaron gida wanda yayi sanadiyyar nasarar da kungiyar kwallon kafa ta Portugal ta samu bisa kan kungiyar kwallon kafa ta Faransa.

An canza Ronaldo a sakamakon raunin da ya samu a gwiwarsa a cikin minti 25 na fara wasan, koda shike wasan yaja hanakalin ‘yan kallo musamman yadda duka kungiyoyin biyu sukai ta kokarin kaiwa juna farmaki.

Kungiyar kwallon kafa ta Portugal ta sami dama kwarai bayan hutun rabin lokaci amma sai dai kash! Sun baras da damammaki da dama da suka samu.

Wasan dai ya tashi da kwallo guda da babu inda kungiyar kwallon kafa ta Portugal ta yi nasarar lashe wannan gasa kuma ta daukin kofin na Euro 2016.