Afghanistan Tayi Maraba Da Shirin Amurka A Kasar

Sai dai kwararru na ganin shirin shugaba Obama ya bar baya da kura

A yau Alhamis shugaban kasar Afghanistan Ashraf Ghani, yayi maraba da shirin shugaba Barack Obama, na barin sojojin Amurka 8,400 suci gaba da kasancewa a Afghanistan har zuwa karshen wa’adinsa.

Sai dai kwararru na ganin shirin shugaba Obaman ya bar baya da ‘kura domin babu masaniyar yadda harkar tsaro zata kasance, musamman da yake lamarin tsaron na kara tabarbarewa.

A baya Gwamnatin Obama tayi shirin rage yawan sojojin Amurka a Afghanistan daga 9,800 zuwa 5,500 kafin karshen wannan shekarar ta 2016 da muke ciki.

Amma a jiya Laraba shugaba Obama ya fitar da sanarwar cewa har yanzu akwai matsalar tsaro a Afghanistan saboda haka zai bar karin sojoji fiyeda yadda aka tsara a baya har zuwa karshen wa’adinsa na shugabancin Amurka ranar 20 ga watan Janairun shekara ta 2017.