Mukaddashin Kaftin din Blackstars Andre Dede Ayew, ya bayyana amincewarsa da wasannin kwallo da ake shiryawa a karshen kowane watan Ramadan wanda akewa lakabi da kofin Sheikh Sharubutu, inda Dede Ayew yayi kiran ga yanuwa musulmi da suyi riko da kyawawan hali da muka koya a cikin Azumin Ranamadan don zama cikin hadin kai da zaman lafiya a kowane lokaci.
Yace ya bada goyon bayana ga wannan gasar na ci kofin Sheikh Sharubutu, ne saboda murnar shagalin bayan Azumi ne dake tattaro Musulmin Ghana wuri daya.
Yace Azumin watan Ramadan lokaci ne mai kyau da muka koyi darasi da dama inji Dede Ayew.
A nasa bangare kuwa, dan wasan tsakiya Mubarak Wakaso ya gargadi matasan Zango da su guji rigima a lokaci da za’a gudanar da zabe a kasar.
Ya ja hankalin matasa dasu hada kai saboda zaman lafiya, ya kara da cewa yakamata ‘yan uwa a daidai wannan lokaci da kasar take shirin yin zabe, a yiwa juna adalci, da kuma kiyaye kawunan mu.
Mai tsaron gidan Blackstars Razak Brimah shima ya yabawa wasannin kofin Sheikh Sharubutu ya kuma yi kira ga jama’a da su taimakawa wasan saboda damace da zata haifar da alheri da yawa.
Yace wannan abu ne mai kyau saboda babban manufar itace hada kan al’ummar Zango da tabbatar da zaman lafiya a lokacin bukin Sallah karamar.
Dan wasan baya Baba Abdul-Rahaman da dan wasan gaba Jordan Ayew duk sun bayyana goyon bayansu ga wasan saboda muhimmanci sa.