Dalibai A Makarantar Amurka A Nijer Sun Rera Wakar Taken Kasar A Bukin Cika Shekaru 240 Da Samun 'Yancin Amurka

A jamhuriyar Nijar kuma, wasu dalibai dake karatu a makarantar kasar Amurka a jamhuriyar Nijar sun raira wakar taken kasar ta Amurka a yayin da ake gudanar da wani kasaitaccen buki domin tunawa da zagayowar ranar 4 ga watan Yuli da kasar Amurka ta cika shekary 240 da samuun ‘yancin kai daga turawan mulkin mallaka.

Jama’a da dama ne suka halarci wannan buki da aka gudanar a ofishin jakadancin Amurka dake jamhuriyar ta Nijar.

Tun a shekarar da jamhuriyar Nijar ta sami ‘yancin kanta, kasar Amurka ke taimaka mata ta hanyoyi da dama, lamarin da ya kara karfafa huldar diplomasiyya tsakanin kasashen biyu kamar yadda jakadiyar Amurka dake a jamhuriyar Nijar ta bayyana a jawabinta na ranar indifenda.

A cikin jawabin nata, ta tabo maganar tsaro da kasar Nijar ke fuskanta da kuma irin rawar da kasar Amurka ke takawa domin tallafa mata do horo da kayan aiki, tare da hikimomin zakulo bayanan sirri domin kyautata tsaro. Ta kuma jinjinawa iyalai da ‘yan uwa da kuma sojojin Nijar musamman kan yaki da ta’addancin da suke fama dashi.

Bayan ‘yan rajin kare hakkin dana dam dana demokaradiyya da shuwagabannin rukunonin jamhuriyar Nijar da suka halarci bukin na cika shekaru 240 da samun ‘yancin kan Amurka, ministocin gwamnatin Muhammadou Yusuf ma sun halarci wannan buki domin bayyanawa Amurka amincewa da irin kokarin da kasar ta sa a gaba.

Saurari Cikakken Rahoton A Nan.

Your browser doesn’t support HTML5

Dalibai A Makarantar Amurka A Nijer Sun Rera Wakar Taken Kasar A Bukin CIka Shekaru 240 Da Samun 'Yancin Amurka