Argentina Tayi Kacha Kacha Da Amurka

Argentina

A wasan kusa da na karshe a gasar Copa America Argentina tayi kacha kacha da Amurka da ci hudu da nema, kasar Chile mai rike da kofin a yanzu haka ta lallasa kungiyar kwallon kafa ta Columbia da kwallaye biyu da nema wanda hakkan ke nuni da cewa Argentina da Chile ne za suyi karon batta a wasan karshe.

Duk kasashen biyu sun fito ne daga rukuni daya wato rukunin “D” a yayin bugawa a rukunin Argentina ta doke Chile biyu da daya, sai dai a shekaru biyu da suka wuce a gasar ta Copa America, wasan karshe an buga ne tsakanin kungiyar wasan kwallon kafa ta Chile da ta Argentina a shekarar 2014, inda Chile ta samu nasara akan Argentina sakamakon bugun daga kai sai mai tsaron gida.

A gasar nahiyar Turai kuwa an buga tsakanin Hungary da Portugal inda aka tashi kunnen doki uku da uku sai Ireland ta doke Australia, biyu da daya sai Italy ta sha kasha a hannun Iceland daya da nema sai kuma Sweden da ta sha kasha a hannun Belgium.

Your browser doesn’t support HTML5

Argentina Tayi Kacha Kacha Da Amurka - 2'49"