Wani Bom Ya Tashi A Wajen Ofishin ‘Yan Sandan Turkiyya

Mutane kamar talatin sun jikkata kuma an tura motocin jinya da dama wurin da abin ya faru

An kashe wani dan sanda guda da wasu fararen hula guda biyu a lokacin da wani bom ya tashi a mota a wajen ofishin ‘yan sandan Turkiyya, kusa da iyakar ta da Siriyya, a cewar Firayin Ministan Turkiyyar, Binali Yildirim yau Laraba.

Mutane kamar talatin sun jikkata kuma an tura motocin jinya da dama wurin da abin ya faru a garin Midyat, a kudu maso gabashin kasar inda kurdawa suka fiyawa.

Firayin ministan ya zargi ‘yan bindigar kurdawa da kai harin. ‘Yan kungiyar kurdawa da ake kira PKK a takaice, sun sha auna jami’an ‘yan sanda da sojan Turkiyya tun daga watan Yulin bara a kokarin da suke yi na samun yankin cin gashin kansu a kudu maso gabashin kasar.

Firayin minista Yildirim yayi wannan jawabin ne bayan da ya ziyarci wadanda suka jikkata a harin da aka kai a Istanbul, inda aka hallaka mutane 11, ciki harda jami’an tsaro su 7, tare da raunata wasu su 36 a lokacin da mutane ke hada-hadar fita zuwa wuraren aiki da safe.