Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya Tana Kashe Kimanin Naira Miliyan Dubu 100 Kan Jinya A Kasashen Waje


Kakakin shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari yace tafiyar da shugaban kasar yayi zuwa London jiya Litinin bata da nasaba da rashin lafiya, a maimakon haka hutu ya tafi.

Femi Adesina, wani babban mashawarcin shugaban kasa kan harkokin sadarwa yace, shugaba Buhari zai yi amfani da hutun wajen duba lafiyarsa da kuma bincika wani matsanancin ciwon kunne da yake fama da shi.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da mataimakin shugaban kungiyar ma’aikatan jinya na kasashen renon ingila ya bayyana takaici kan tafiyar kwana goma da shugaban kasar ya yi zuwa ingila da cewa, cin fuska ne ga kwararru da kuma kimar kasar.

Likita Osahon Enabulele yace, Najeriya tana kashe kimanin dala miliyan dubu dari, kan jinya a kasashen waje, musamman kan ‘yan siyasa da kuma masu rike mukaman gwamnati da mataimakansu dake masu rakiya.

Yace shugaba Buhari ya yi watsi da damar da yake da ita ta sauya lamarin wajen yin jinya a Najeriya.

Sai dai kakakin shugaban kasar Adesina yace wadansu likitoci biyu sun duba lafiyar shugaba Buhari kafin suka shawarce shi ya je kwararru su sake duba lafiyarshi, yayinda tafiyar da ya yi London.

Likita Osahon Enabulele yace, shugaba Buhari zai karawa likitocin kasar karfin guiwa idan aka yi jinyarshi a gida, inda ake da kwararru da suke iya buga kirji da takwarorinsu na kasashen duniya ko ma sufi su kwarewa.

Adesina yace shugaba Buhari yana da kwarin guiwa kan
kwarewar likitocin Najeriya.

XS
SM
MD
LG