Kungiyar ‘yan bindigar Niger Delta,masu suna (Avengers) tace ta kai wani sabon hari a wata matattaran danyen Mai dake yankin na Niger delta, mallakar Chevron na kasar Amurka dake yankin na Niger Delta.
A wata sanrwa da kungiyar ta fitar wannan harin dai kamar yadda masu lura da alamura kan tsaro suka bayana ya nuna yadda kungiyar take amfani da wasu fannonin zamani wajen kai hare hare.
Yanzu dai hare haren sun tsanata matuka da kuma haifar da barna mai yawa kan bututu mai a yankin na Niger Delta.
Wani tsohon ma’aikacin mai a yankin na Niger Delta, Mu’azu Magaji, yace bangaren mai bangare ne mai mahimmancin gaske a kowace kasa saboda dinbin dukiyar dake tattare da ita saboda haka ya zama wajibi jama’a su fahimci cewa shugaban kasa yana da dama da zai kare lafiya da dukiyar jama’a da na kaza.
Ya kara da cewa wasu kafanoni suna iya nema tashi baki daya daga kasar saboda fitinar ta yi yawa da kuma rigingimu.
Akwai dai karuwar damuwa mai yawa tsakanin kafanonin aikin hakar danyen mai bisa la’akari da wa’adin da kungiyar ta Avengers, ta bayar na ranar 26, ga wannan watan da muke ciki cewar kafanonin hakar mai da suke yankin su kwashe kayansu su bar yankin.
Your browser doesn’t support HTML5