Firayin ministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya kara yawan ministocinsa dake cikin gwamnatin shi ta hadin guiwa, amma nadin wani mutum mai ra’ayin rikau a matsayin dan majalisar ministocin kasar ya janyo suka, daga cikin kasar da ma wajen ta.
Netanyahu ya rattaba hannu a yarjejeniyyar hadin guywar ne a Knesset, majalissar Isra’ila, tare da sabon ministan nashi da aka yi ta takaddama a kansa, Avigdor Lieberman, wanda ke ya shugabantar jam’iyyar Yisrael Beitenu.
Liberman yana daya daga cikin mutanen da suka yi kaurin suna saboda irin lafazin batanci da yake anfani da shi a jawabansa kuma yana da ra’ayin rikau sosai game da Paladinawa. Zai yi aiki a matsayin sabon ministan tsaron kasar, inda zai taka muhimmiyar rawa wajen fidda muhimman manufofin kasar akan tsaro, yaki da zaman lafiya.