Tsohuwar Sakatariyar Harkokin Wajen Amurka Hillary Clinton da abokin karawarta a yakin nemar zama dan takarar Shugaban kasa karkashin jam'iyyar Dimokarat, Sanata mai wakiltar Vernon Bernie Sanders, sun raba jahohi biyu wajen yakin neman zabensu, ta yadda Hillary Clinton ta dada kusa da zama 'yar takara cikin makwanni 3 masu zuwa.
Clinton ta dara Sanders da kuri'u 2,000 a jahar Kentucky, mai samar da gawayin kwal. Tazarar ta yi kankanta ta yadda ma jami'an zaben su ka ce ba za su yi gaggawar bayyana wanda ya ci a hukumance ba, to amma Clinton ta ce ita ta yi nasara, karo na farko tun bayan watan Mayu. A halin da aka ciki kuma Sanders ya yi galaba kanta a jahar Oregon da ke gabar Tekun Pacific.
Bayan sakamakon na jahohi biyu, yinkurin Clinton na zama Shugabar kasar ta farko mace, zai kai ga zamanta 'yar takara ranar 7 ga watan Yuni, bayan da jahohi 6 su ka kada nasu kuri'un. Bayan nan Dimokarat na iya ayyana ta a matsayin 'yan takara a babban taron jam'iyyar da za a yi a watan Yuli.