Majalisar sarakunan makafin jihar ta nuna rashin jin dadi da matakin na gwamnatin jihar akan hana barace barace.
Alhaji Muhammad Rabiu Abdullahi sarkin makafin Minna kuma shugaban majalisar sarakunan makafin jihar yace sun taru ne ba wai su kalubali dokar ba ne. Yace sun karbi dokar amma a yi masu adalci.
Maganar tura masu 'yansanda su kamasu su bugesu da 'ya'yansu da jikokinsu a kasarsu bai dace ba. Batun yi masu tanadi ba yau aka fara ba amma tanadin da suka gani yanzu na kamesu shi ne ya damesu, inji Alhaji Muhammad Rabiu sarkin makafin Minna.
Yace kafin a fara kamasu daga ranar 23 na wannan watan wajibi ne a basu aiki saboda duk wanda ya kamata ya yi aiki ya je ya yi.
Taron makafin ya hada har da hadaddiyar kungiyar makafi ta jihar. Malam Abdurahaman Awal Bidda shi ne shugaban kungiyar makafin kuma ya yi furuci. Yace gwamnati ce ta cinna masu wuta domin zaune suke aka zo aka ce akwai sabuwar doka da zata hana makafi bara. Yace duk 'yancin da yake nasu gwamnati ta basu. Abun da ya fi basu haushe har yana sasu hawaye shi ne gwamnati bata muamala dasu kamar 'yan Adam. Da tana muamala dasu kamar mutane to ko idan za'a yi abu akansu za'a tuntubesu.
To saidai gwamnatin jihar tace ta dauki matakin ne domin shawo kan yawon barace barace da ya addabi sassa da dama na Najeriya. Tace tayi tanadi domin kyautatawa nakasassun. Sakataren yada labaran jihar Jibril Baba Ndace yace a bangaren nakasassun akwai matakan da ta dauka kamar gidajensu inda zasu zauna.
Ga karin bayani.