‘Yan kungiyar ISIS sun kashe akalla mutane 49 ciki har da mayakan da suka kame, da ‘yan adawar siyasa, da kuma wasu da aka zarga da maita, tun watan Fabarairun shekarar da ta gabata a birnin Sirte dake gabar tekun Libya, wuri da ya zamo tunga mafi karfi ga mayakan, a wajen Siriyya da Iraki, a cewar rahoton wata kungiyar kare hakkokin bil’adama ta kasa-da-kasa.
A cewar kungiyar ta Human Rights Watch, mayakan kungiyar ISIS sun yi ta satar mutane kuma mayakan Libiya da aka kame sun bace a garin Sirte, da yawansu ma ana jin sun mutu.
A sauran garuruwan da ‘yan ISIS suke rike da su kuma kungiyar ‘yan jihadin sun kafa shari’ar musulunci mai tsauri a birnin na Sirte, inda suke sa ido a harkokin jama’ar garin na yau da kullum -kama daga tsawon wandon da maza za su sa, da kalar kayan da mata za su sanya, da kuma umurni da za a ba dalibai a makarantun gwamnati a cewar kungiyar kungiyar sa idon.
Mayakan basa samarwa jama’ar muhimman abubuwan rayuwa, a cewar kungiyar. Maimakon haka su kan karkata akalar abinci, magunguna, man fetur, kudi da kuma gidajen da suka mallake daga wadanda suka tsere, zuwa dumbin mayakansun da suka kai kusan 1,800 a birnin.