Kungiyar Kwadago Ta Gudanar Da Zanga Zangar Lumana A Lagos

Nigeria Oil Crisis

Sai dai a bangare guda wata kungiya tace bata goyon bayan zanga zangar

kungiyar kwadago ta NLC tasha alwashin gudanar yajin aikin gama gari na sai baba ta gani a Najeriya sakamakon karin farashin albarkatun man fetur da gwamnati tayi. Kungiyar ta hana zirga zirgan ababen hawa a harabar Filinjirgin sama na kasa da kasa a Lagos.

A lokaci wannan zanga zanga na lumana dai shuwagabani daban daban na kungiyar kwadagon sunyi jawabi ionda suke jaddada cewa wannan yajin aiki ba gudu ba jada baya sai dai idan Gwamnati ta rage farashin albarkatun Man fetur da ta kara kamar yadda suke cewa.

Suka ce an dade ana ci da bazar talaka a Najeriya, kuma lokaci yayi da zamu yi tawaye mu nuna cewa bamu yarda ba, canjin da za’a yi mana kennen, wanna ba shine canjin da talakawa suka zaba ba don haka muna kira ga Gwamnatin Muhammadu Buhari da ta duba wannan alamari ta kuma maida tsohon farashin kamar yadda yake ada.

Komrade Waziri na kungiyar arewacin Najeriya, na daya daga cikin wadannda suka yi jawabi, kuma yace dalilin wannan yajin aiki shine na halin da ‘yan Najeriya ke ciki da kuma Karin kudin mai daya taso a lokacin da ba’a zataba saboda ana cikin kunci .

Sai dai a bangare guda Alhaji Ado Dansudu shugaban wata kungiya ta ‘yan arewacin Najeriya, a Lagos, yace basu goyon bayan wannan yajin aiki, yana mai cewa da aka cire tallafin man sai gashi ana samun mai a gidajen mai amma kafin a cire tallafin ana sayen man har Naira dari biyu lita daya.

Your browser doesn’t support HTML5

Kungiyar Kwadago Ta Gudanar Da Zanga Zangar Lumana A Lagos - 3'41"