Wani sabon rahoto kwanan na kungiyar kare hakkokin bil’ Adama ta Amnesty International, ya ce kusan mutane 150 ciki har da yara wadanda shekarunsu ba su kai 6 ba suka mutu a lokacin da suke tsare hannun sojoji a arewa maso gabashin Najeriya cikin shekarar nan.
Kungiyar Amnesty International ta ce ‘yan kananan yara, na cikin mutane 149 din da aka sami rahoton mutuwarsu a gidan yarin barikin Giwa, wani gawurtaccen wajen tsare mutane a birnin Maiduguri wanda kungiyoyin kare hakkokin bil’adama suka caccaka a baya.
A wannan barikin ne ake tsare wadanda ake zaton ‘yan Boko Haram ne, kungiyar da ta yi sanadiyyar mutuwar kiyasin mutane 20,000 a arewa maso gabashin kasar cikin shekaru 8.
A wata sanarwa daraktar nazari ta kungiyar Amnesty International mai kula da harkokin nahiyar Afrika, Natsanet Balay, ta ce ya zama dole a rufe wannan gidan yarin ba tare da bata lokaci ba haka kuma a saki duk ilahirin wadanda ke tsare ko kuma a kai su wuraren.
Sai dai rundunar Sojan Najeriya ta musanta wannan binciken da kungiyar Amnesty ta yi. Mai magana da yawun rundunar Rabe Abubakar ya ce sun ba jami’an kungiyar Amnesty damar shiga barikin Giwa da kuma wasu wuraren da ake tsare mutane a arewa maso gabashin Najeriya a shekarar da ta gabata haka kuma sun yi canje-canjen da kungiyar ta basu shawarar su yi.
Rahoton na kungiyar Amnesty wanda ya fito yau Laraba, ya fadi cewa yanzu haka barikin Giwa na dauke da mutane 1,200, yawancinsu kuma a wajen sumame aka kama su kuma suna tsare ba tare da an yi masu shari’a ba. Mutane 120 din da ke tsare yanzu haka, yara ne.