Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Buhari Ya Fusata Da Furucin Cameron


Hoton Frayin ministan Ingila David Cameroon,raanr litinin a wani taron manema labarai a fadar shugaban kasar Ingila.
Hoton Frayin ministan Ingila David Cameroon,raanr litinin a wani taron manema labarai a fadar shugaban kasar Ingila.

A dai dai lokacin da shugaba Mohammadu Buhari ya isa kasar Ingila, domin halartar kasaitaccen taro na kasa da kasa akan yaki da cin hanci da karbar rashawa.

Yau Fara Ministan Ingila David Cameron, ya kai ziyarar ban girma ga sarauniyar kasar, wanda ya samu rakiyar kakakin Majalisar kasar da ma wasu kusoshin gwamnati, inda aka ji David Cameron yana radawa sarauniyar Ingila, cewa za a yi taron da zai sami halartar kasashe biyu dake kan gaba a matsalar cin hanci da karbar rashawa wato Najeriya da Afghanistan.

Wannan bayani dai yanzu haka na ciwa Najeriya Tuwo a kwarya, kuma tuni fadar gwamnati ta nuna damuwarta akan wannan bayani da David Cameroon yayi.

Mallam Garba Shehu, kakakin shugaba Buhari ya bayyana, inda yace tabbas wannan magana tayiwa Najeriya ciwo domin ba ayi la’akari da irin gagarumin aiki da shugaba Mohammadu Buhari yake yi ba, wajen yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya.

Saurari cikakken rahotan.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:28 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG