Yayin da hankula suka fara kwantawa biyo bayan tashin hakalin da akayi a tsakanin al’umar Wurkum da Shomo, a kananan hukumomin Karim Lamido da Lau, lamarin da ya kai aka sami hasarar rayuka da kuma kona fiye da gidaje dubu daya.
Yanzu haka dai al’umomin wadannan kananan hukumomi sun sasanta, biyo bayan wani taron sulhu da aka gudanar inda daga bisani suka fitar da sanarwa na hadin guiwa na yafewa juna.
Hon. Tanko, na bangaren Wurkum, yace abinda ya kawo wannan takardan shine dattawan Wurkunawa ne suka ce wanna fadan basu santa ba kuma basu san inda ta fito ba kuma babnu dalilin, kuma wani mataki ne za’a dauka da gaggawa domin kawo karshen wannan fadan ana ciki haka sai sai ga dattawan Shumawa, suka ce sun zo ne da rokon cewa ayi gaggawan hada kai domin dakatar da wannan fadan.
Shima dai Malam Abubakar Shomo, yace a gaskiya dattawan Shomo da na Wurkum, sun tattauna domin kawo karshen wannan tashin hankali.
Your browser doesn’t support HTML5