An Alakanta Mohammed Abrini Da Hare-Haren Birnin Paris

Harin Paris

Harin ya yi sanadin mutuwar mutane 130, da raunata fiye da wasu 350

Masu gabatar da kara a kasar Belgium sun fadi yau Talata cewa sun tuhumi karin mutane 2 game da harin da aka kai watan jiya a Brussels, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane 32.

Wani bayanin da ya fito daga ofishin babban mai gabatar da kara na gwamnatin tarayya ya bayyana mutanen da ake tuhumar da Smail F da kuma Ibrahim F, da cewa su na da hannu a hayar gidan da mai yiyuwa daya daga cikin maharan na Brussels ya yi amfani da shi a matsayin mabuya.

Haren-haren sun hada da wasu tagwayen hare-haren da aka kai filin jirgin saman Brussels da wani harin bam din kuma a wata tashar jirgin kasa da ke Brussels.

'Yan sanda sun kama mutane 6, ciki har da Mohammed Abrini, wanda aka ganshi ganga da 'yan kunar bakin waken biyu a bidiyon kamarar filin jirgin saman.

Ana kuma alakanta Abrini da hare-haren da aka kai birnin Paris a watan Nuwamba, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane 130. Masu gabatar da karar sun ce dama maharan na Brussels na shirin sake kai hari kan Faransa ne, to amma sai su ka yanke shawarar kai hari maza-maza a Brussels bayan kama wani jagoran harin na birnin Paris, Salah Abdelsalam.