Binciken jin ra’ayin da kamfanin dillancin labarai na Associated Press ya gudanar, ya ji ra’ayoyin mutane 1,076 a tsakanin watan Maris da Aprilu.
Kuma kashi 21, sun ce lallai Sanders za su jefawa kuri’a, yayin da kashi 41 suka ce akwai yiwuwar duba zabin na Sanders.
Ita dai Hillary Clinton da ta fi samun karbuwa a jam’iyar ta Democrat, ta zo ta biyu a binciken, yayin da a bangaren Republican Ted Cruz da John Kasick duka suka samu kashi 43 a bangarori biyu, sannan Donald Trump ya zo na karshe da kashi 35 a bangarori biyu da aka ji ra’ayin mutanen.