Idan Aka Fara Lura Dasu A Najeriya Kasashen Duniya Zasu Kawo Taimako

Yara Kurame

Idan aka dasa masu dodon kunne zasu iya ji kuma za’a koya masu Magana.

Gaskiya ina ganin ba daidai bane a rika abatar kurame da mutane masu nakasar ji ba dan ya nuna tafkar ba za’a iya samamasu magani ba, ni ina gani yafi dacewa a kira su mutane masu kalubalen rashin ji.

Minista kiwon lafiya na Najeriya, Farfesa Isaac Adewale, ne ya furta haka a wurin wani kwarya kwaryar taro da wasu yara kurame a ofishin sa karkashen wata kungiya daga Kano, dake aikin tallafawa kurame.

Ministan ya bukaci jami’an kungiyar da su rubuta duk bukatun irin wadannan yara domin zai kafa wani kwamiti a ma’aikatar lafiyar da zai rinka duba lamuran kuramen don tallafawa masu.

Daya daga cikin kuramen dake amsar magani da mahaifiyar sa Hajiya Aisha, da ta rako shi tace yana fuskantar matsalar rashin ji da kuma rashin Magana, amma tace likitan dake kula dashi da sauran yaran yace idan aka dasa masu dodon kunne zasu iya ji kuma za’a koya masu Magana.

Ibrahim Garba shugaban kungiyar tallafawa kuramen yace kamar yadda jihar Kano, ta kawo dauki na gwajin yaran aka gano wadanda suke bukatar irin wannan aiki suma yanzu Gwamnatin tarayya da aka kawo masu wannan bukata sun ammince.

Kuramen dai a cewar Dr. Sulaiman Abdu, dake kula da lallurar su yace zasu iya samun warkewa amma aiki zai kusan Naira miliyan 6, ko wane kurma. Ya kara da cewa matukar aka fara wanna akwai kasashen duniya da kungiyoyi daga wajen zasu agaza.

Your browser doesn’t support HTML5

Idan Aka Fara Lura Dasu A Najeriya Kasashen Duniya Zasu Kawo Taimako 3'19"