Yau shugaba Muhammadu Buhari, da tawagarsa suka bar Najeriya, zuwa kasar Amurka domin domin hadewa da shuwagabanin kasashen duniya karkashin shugabancin shugaban Amurka, Barack Obama, domin yin nazari akan amfani da makamashin Nuclear.
Kasashen zasu yi mahawara domin yin matsayin da zai taimakawa kasa da kasa kuma yayi kariya daga fitittunu na zamani da ake fuskanta a yanzu.
Farfesa Nok Jonathan Andrew, kwararre akan sha’anin makamashin Nukiliya, yace Najeriya babbar kasa ce a Afirka, kuma tana da hujjar hallartar taron domin tufa albarkashin bakinta akan manufofi da bukatun da take da na amfani da wannan makamashin domin inganta rayuwar al’umar ta.
Ya kara da cewa kamar cibiyar biniciken makamashi na jami’ar Ahmadu Bello, akwai kwararru sosai da suka hazaka a koyon ilimin makamashi Nukiliya, kuma suna horas da jama’a, a Ghana, Afirka ta Kudu dama Amurka.
Your browser doesn’t support HTML5