A yau ne ranar da majalisar dinkin duniya ta ware domin fadakarwa akan cutar tarin fuka, tun a shekarar 1982, ne dai hukumar Lafiya ta duniya ta kaddamar da ranar 24, ga watan Maris, na kowace shekara domin fadakarwa game da cutar na tarin fuka.
A wasu alkalluma da hukumar Lafiya ta duniya ta fitar ya nuna cewa mutane miliyan tara da dubu dari shida ne suka harbu da cutar ta tarin fuka a shekara ta 2014, yayin da a ciki mutane miliyan daya da rabi ne cutar ta hallaka.
Jami’an kiwon lafiya a jihar Neja, a taryyar Najeriya, sun gudanar da jerin gwano domin fadakar da jama’a, game da wannan cutar na tari fuka.
Kwamishinar lafiya na jihar Neja, Dr. Mustapha Jibril, yace idan har mutun yaga tari ya wuce mako biyu bayan yayi amfani da maganin tari toh yayi tunanin kila tarin fuka ne, ko kuma yawan yin gumi ko tari da jini ko rama ko kuma yawan zazzabi duk yana cikin alamun tarin fuka, sai a nufi asibiti.
A jihar Neja, dai mutane dubu daya da dari shida da goma sha daya ne suka kamu da cutar a shekarar data gabata daga ciki mutane dari tawas da tamanin da uku ne aka yiwa magani sannan mutane sitin da shida suka mutu yayi da mutane ashirin da hudu suka tsere daga wurin sha magani.
Ma’aikatar lafiya ta jihar Neja, ta tabbatar da cewa akwai wurin gwaji da bada magani kyauta ga duk wanda ya kamu da cutar tarin fuka.
Your browser doesn’t support HTML5