Yau Shugaba Muhammadu Buhari ya bude wani taron bita na kwanaki biyu akan tattalin arziki wanda ya samu halartar Gwamnoni da Ministoci da sauran masu fada aji a sha’anin gudanar da mulki na Najeriya.
Shugaban Muhammadu Buhari, yayi amfani da wannan lokacin wurin yiwa ‘yan Najeriya bayani akan abubuwan da Gwamnatin sa tasa a gaba dangane da farfadowa da tattalin arzikin kasa.
Yace sha’anin Noma shine kan gaba ganin faduwar da darajan mai fetur yayi a duniya, kuma ya kasance tilas ne Najeriya yanzu ta dawo turbar a Noma, domin ta nan ne Najeriya ke samun kudi shiga shekarar 1950.
Gwamnan jihar Adamawa Bindo Jibrila, wanda ya yiwa muryar Amurka Karin bayani yana mai cewa Gwamnatin jihohi da Gwamnatin tarayya zasu hada kai ne wajen ganin cewa an samarda kudaden ta babban bankin Najeriya, ga manoma da ruwan kudaden dan kalilan ne kuma za’a taimaka wajen sayarda amfanin idan an noma ta yarda biya kudi ba zai kawo damuwa ba.
Your browser doesn’t support HTML5