Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kwango Zata Rufe Layukan Sadarwa Na Kwana Biyu Saboda Babban Zaben Kasar.


Shugaba Denis Sassou N'Guesso na jamhuriyar kwango.
Shugaba Denis Sassou N'Guesso na jamhuriyar kwango.

Ministan harkokin cikin gidan kasar ne ya bada wannan umarni cikin wasika da ya aikewa kamfanonin sadarwa biyu da suke aiki a kasar.

A jamhriyar kwango, gwamnatin kasar ta umarci kamfanonin sadarwa da suke kasar su katse dukkanin hanyoyin sadarwa gobe lahadi, lokacinda kasar take zaben shugaban kasa.

Ministan harkokin cikin gida na kasar Raymond Zephrin, ya aike da wasika zuwa ga manyan kamfanonin sadarwa biyu da suke aiki a kasar cewa, saboda dalilan tsaro, tilas su dakile dukkan hanyoyin sadarwa ciki harda sakon text, a ranakun lahadi da kuma litinin.

Wasikar, wacce aka gani a internet, ta kuma bada jerin lambobi da zasu ci gaba da aiki yayin da ake zaben.

Wannan umarni zai iya kara kara zaman dar dar a kasar, inda mutumin da ya dade yana mulkin kasar, shugaba Denis Sassou Nguesso, yake sake takara, ind a zai kara da wasu 'yan takara takwas, cik harda tsohon hafsa a rundunar mayakan kasar Janar Jean-Marie Makoko.

XS
SM
MD
LG