Wasu Janar Janar Na 'Yan Tawayen Sudan Ta Kudu Zasu Isa Birnin Juba

Kakakin dakarun ‘yan tawayen, Kanar William Gatjiath Deng, ya ce zuwan Janar-Janar din wata alama ce na aiwatar da shirin da aka shata

Yan tawayen Sudan ta Kudu, sun ce ana sa ran isar wasu Janar-Janar su 23 a birnin Juba a ranar Litinin mai zuwa.

Hakan kuma sharar fage ne na zuwan shugabansu, Riek Machar, wanda aka baiwa mukamin mataimakin shugaban kasa a gwamnatin hadakar da ake shirin kafawa.

A baya Machar ya fadi cewa, ba zai shiga birnin na Juba ba, har sai idan dakarunsa da ‘yan sanda kusan dubu uku sun shiga birnin, tare da karin wasu ‘yan sanda 1,200 a Bor da Malakal da Bentiu.

Shirin aiwatar da matsayar da aka cimma a watan Agustan shekarar 2015, ya kasance yana tafiyar hawainiya, yayin da bangaren ‘yan tawayen da na shugaba Salva Kiir su ke takaddama kan wasu sabbin juhohi 28 da Kiir ya kirkiro.

Haka zalika bangarorin biyu sun yi ta zargin juna da saba shirin tsagaita wutar da aka cimma a baya.

Kakakin dakarun ‘yan tawayen, Kanar William Gatjiath Deng, ya ce zuwan Janar-Janar din birnin na Juba, wata alama ce da ke nuna cewa da gaske suke yi game da batun aiwatar da shirin da aka shata a watan Agustan bara.