Al’amura na neman tsayawa chik, a jihohin Kebbi da Zamfara, a sakamakon matsalar karancin man fetur dake kara ta’azzara a kowace rana.
Matsalar ta shafi kusan dukkan alamuran jama’a nay au da kullum bama kamar jihar Kebbi, inda kasha 80, bisa 100, na jama’ar sun dogara ne da noman rani a zaman hanyar neman abinci.
Wani manomi Alhaji Muhammadu Bello Shattima, yace aikin noman rani bai yuwa batare da man fetur ba, rashinsa kuwa yasa ana ci baya.
Alhaji Umaru direba wani dattijo dake sana’ar sifiri a birnin Sokoto, yace wannan matsalar ta rashin man fetur ta jefa jama’a cikin kuncin rayuwa.
Shi kuwa Abdullahi Nakura Kauran Namoda cewa samun shugaba nagari ba zai isa ya wadatar da Najeriya ta gyaru ba sai kai kanka dan kasar ka gyara zujiyar ka, kaso kasar ka, kaso sauran ‘yan uwanka ‘yan kasar Najeriya sannan zamu samu wani ingantatcen ci gaba da kwanciyar hankali.
Sai dai dilalalan man fetur suna musanta hannun su a cikin wannan matsalar kamar yadda Sulaiman Magaji AP, shugaban dilalan man fetur masu zaman kansu yake cewa rashin wadatar man shi ya kawo karancin sa yace afi baiwa manyan garuruka mahimmanci wajen rabon man kamar su Lagos da Abuja.
Your browser doesn’t support HTML5