Gwamnan Jihar Lagos Akinwumi Ambode ya baiwa mazauana wasu rukunin gidaje dake anguwan Lekki na masu hannu da shuni Izinin ficewa daga gidajen da suke ciki domin gudanar da binciken Ingancinsu. Gwamnan ya bada wannan umarni ne bayan mutuwan mutane 34 a wani gini a yankin a makon jiya.
Gwamna Ambode yace duk wani gida da aka samu ba yada ingancin da doka ta tanada za’a rushe shi, tuni dai Gwamnan ya bada umarnin sauke shugaban hukumar kula da ingancin gine gine da tsara biranai da wasu jami’an sa sakamakon samun su da sakaci a aiyukansu.
Architect Kabir Ahmed Abdullahi, tsohon shugaban hukumar tsara biranai ne a Lagos, kuma mai baiwa Gwamna shawarwari akan harkokin samarda ruwan sha a Lagos, yace dalilan sallamar jami’an daga aiki shine domi Gwamnati ta sami shuwagabanin hukumar da laifin yiwa aikinsu rikon sakainar kashi.
Rugujewar gidaje dai ba sabon abu bane a Najeriya masamman ma dai a jihar Lagos, domin ko a shekarun baya wani gidan sama mallakar Cocin T.B Joshua, ya ruguje tare da kjashe mutane fiye da dari akasarinsu ‘yan kasar Afirka ta kudu.
Your browser doesn’t support HTML5