Kungiyoyin Adawa A Sudan Ta Kudu Sun Amince Da Shirin Kai Dakarun ‘Yan Adawa 1,370, Juba

Haka kuma ana sa ran wasu jami’an tsaro za su hade da su bayan an kafa gwamnatin ta hadin guyawa

Kungiyoyin adawa da ke tattaunawar samar da zaman lafiya a babban birnin kasar, don shirin zuwan shugaban ‘yan tawaSudan ta kudu sun amince da shirin kai dakarun ‘yan adawa 1,370 a Juba,yen Riek Machar don kafa gwamnatin gamin gambiza a kasar.

Wata hukumar sa idon Sudan ta kudu ta fada a wata sanarwa jiya Talata cewa, ana sa ran yan sanda da sojoji da ke goyon bayan ‘yan adawa za su je birnin na Juba ba tare da bata lokaci ba.

Haka kuma ana sa ran wasu jami’an tsaro za su hade da su bayan an kafa gwamnatin ta hadin guiwa.

Biyo bayan shekaru 2 da aka kwashe ana yakin basasa a kasar, shugaban ‘yan tawaye Riek Machar da shugaban Sudan ta Kudu Salva Kiir sun rattaba hannu a wata yarjejeniyar kawo zaman lafiya a watan Agustan bara, inda suka amince za su kafa gwamnatin hadin guiwa ta tsawon watanni 30 kafin a yi zabe. Kiir ya nada Machar a matsayin mataimakinsa a makon da ya gabata, wani mataki na farko akan shirin kafa gwamnatin.

Duk da wannan matakin na kawo hadin kai, an cigaba da fada a wasu sassan Sudan ta Kudu. A cikin shekaru 2 da suka gabata, dubban mutane sun mutu kuma fiye da mjiliyan 2 suka kauracewa muhallansu.

Ana sa ran sakataren MDD Ban KI-moon zai je Juba ranar Alhamis, inda zai gana da Kiir ya kuma je sansanin MDD inda aka ajiye farar hular da rikicin ya shafa.