Ana sa ran nan da jumma’a Sauran kungiyoyi za su bayyana ko su na ciki ko a’a.
WASHINGTON, DC —
Shugaban kasar Siriyya Bashar al-Assad ya tabbatarwa takwaranasa na kasar Rasha Vladimir Putin cewa Siriyya ta shirya aiwatar da yarjejeniyar tsagaita wuta da aka shirya za ta zai fara aiki ranar Asabar.
Shugabannan biyu sun gana ta wayar tarho yau laraba kuma sun bayyana muhimmancin cigaba da yakar kungiyoyin ‘yan ta’adda kamar su ISIS da Jabhat al-Nusra. Sai dai mayakan sa kan ba sa cikin kudirin tsagaita wutar da Amurka da Rasha su ka gabatar. Ana sa ran nan da jumma’a Sauran kungiyoyi za su bayyana ko su na ciki ko a’a.
Kwamitin shawarwarin ‘yan adawa ya ce shigarsa cikin yarjejeniyar na da muhimmanci don kai taimakon jinkai da kuma kawo karshen mamaya da kai hare-hare ta sama akan farar hula.