Ana Ci gaba Da Kada Kuri’u a Zaben Jamhuriyar Nijar a Cikin Kwanciyar Hankali

Da misalin karfe goma na safe ne shugaban jamhuriyar ta Nijar Muhammadou Issoufou, ya isa wajen jefa kuri’a

Ana ci gaba da kada kuri’u a zaben jamhuriyar Nijar a cikin kwanciyar hankali koda yake an dan sami jinkiri a wurare da dama saboda rashin isar kayan aiki da wuri.

Da misalin karfe goma na safe ne shugaban jamhuriyar ta Nijar Muhammadou Issoufou, ya isa wajen jefa kuri’a, daga nan sai shuigaba Issoufou Muhammadou yayi ‘yar takaitacen jawabi inda yayi kira ga ‘yan kasa dasu tabbatar da cewa an gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali.na mai cewa kowa ya zabe abinda yaga cewa yafi dace wag a kasar.

Itama jakadiyar Amurka a jamhuriyar Nijar, Eunice, ta saga dan gani da ido yadda ake gudanar da zaben tace a yanzu komai na gudana cikin tsari masamman na wannan mazabar koda yake an dan yi jinkiri wurin fara kada kuri’a na dan lokaci.

Your browser doesn’t support HTML5

Ana Ci gaba Da Kada Kuri’u a Zaben Jamhuriyar Nijar a Cikin Kwanciyar Hankali -2'46"