Ayyukan tattalin arziki sun tsaya cik a kasar Chadi da kuma yankin arewacin kasar Kamaru a bayan hare-haren da 'yan Boko Haram ke yawaita kaiwa kan motoci masu jigilar kayayyaki daga Jihar Borno zuwa wadannan kasashen biyu na yankin tsakiyar Afirka.
A ranar asabar da ta shige ma, mayakan Boko Haram sun kwace wasu motocin jigilar kaya guda uku na Chadi tare da kayayyakin dake cikinsu, suka tafi da su wani wurin da ba a sani ba.
Wata mai sayar da kayayyaki a daya daga cikin kantuna mafi girma a N'Djamena, babban birnin Chadi,Nafissa Adja, ta ce har yanzu ba a biya ta albashin watan da ya shige ba, a saboda yanzu an yi wata da watanni kantin bai samu kayayyakin da ya saba samu yana sayarwa daga Jihar Bornon Najeriya ba.
Wani direban babban mota a kasar ta Chadi, Tocba Haman, yace a yanzu ya daina zuwa dauko kaya a Najeriya saboda 'yan Boko Haram su na kai hari a kan motocin suna kashbe direbobinsu.
Yace duk da kasancewar akwai sojoji masu yawa a kan hanyar, 'yan ta'adda su na ci gaba da rike wasu kauyuka.
Wani jami'in kwastam a kasar Chadi, Abdoul Said, yace a ranar asabar da ta shige, wasu kamfanoni guda uku na kasar ta Chadi sun yi hasarar motocinsu na dauko kaya a bayan da 'yan Boko Haram suka kwace su a garin gamboru, wanda wata gada mai tsayin mita 500 kawai ta raba shi da garin Fotokol na kasar Kamaru.
Ya kara da cewa a cikin makonni bityun da suka shige, 'yan Boko Haram sun kai farmaki a kan motocin daukan kaya masu yawa.
Birnin N'Djamena, yana da tazarar kilomita kasa da 50 kawai daga bakin iyaka da Jihar Borno ta Najeriya.
Kasar Chadi da kuma yankin arewacin kasar Kamaru su na samun kayayyaki masu yawan gaske daga Maiduguri, babban birnin Jihar Borno. Ana biyowa da kayayyakin ta Gamboru a tsallaka zuwa garin Fotokol na bakin iyaka a Kamaru, zuwa garin Kousseri dake bakin iyakar Kamaru da Chadi, dab da birnin N'Djamena, inda nan akasarin kayayyakin ke tsayawa.
Daya hanyar da Chadi ke samun kayayyaki ita ce wadda ta taso daga tashar jiragen ruwan Douala a kasar Kamaruy. Amma motocin dake biyowa daga nan ma ba su tsira daga hare-haren 'yan Boko Haram ba idan sun shiga arewacin Kamaru.
A yanzu dai Chadi ta fara dogaro kan makwabciyarta ta arewa, Sudan domin samun kayayyaki. Sai dai rashin kwanciyar hankali a bakin iyakar yammacin Sudan, na haddasa rashin kwanciyar hankali a dukkan kasashen biyu.