Lionel Messi yana iya murmurewa ta yadda zai buga wasan el Clasico ma kungiyarsa ta FC Barcelona a wannan watan, amma kuma shugaban kungiyar, Josep Maria Bartomeu, yace kulob din ba zata tilasta masa ya komo wasa ba.
Messi, dan kasar Ajantina, ya daina wasa tun ranar 28 ga watan Satumba a dalilin jin ciwon da yayi a guiwarsa a lokacin wasan FC Barcelona da Las Palmas.
Barcelona ta samu nasara a wasanni 7 cikin 9 da ta buga ba tare da zakaran nata ba, amma a ranar 21 ga watan nan, zata kara da babbar abokiyar tsamarta Real Madrid a karawar da aka sanya ma suna El Clasico. A yanzu haka dai, FC Barcelona tana gaban Real Madrid da maki uku ne kacal a saman teburin wasannin La Liga.
Bartomeu yace Messi yana murmurewa kamar yadda aka zata tun farko, amma ba zamu tilasta masa komowa filin wasa ba. “Ina fata zai buga (a karawa da Real Madrid). Idan zai iya to, amma idan ba zai iya ba, muna da gogaggun ‘yan wasan da zamu iya doke su” in ji shugaban na kungiyar Barcelona.
Kafin ya ji rauni a guiwarsa, Messi ya jefa kwallaye 6 a wasanni 10 da ya buga a wannan kakar kwallo ta 2015/16.