Hotunan Taron Kolin Kasashen Afirka Da Kasar Indiya A Birnin New Delhi

Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya a lokacin da ya isa zauren taron kolin

Karamin ministan man fetur da gas na Indiya, Dharmendra Pradhan, yana tarbar shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya a lokacin da ya isa zauren taron.

Jami'an kasashen Afirka su na daukar hoto tare da masu masaukinsu na Indiya a ranar farko ta taron kolin Indiya da kasashen Afirka a birnin New Delhi.

Bakin dake halartar taron kolin na Indiya da kasashen Afirka a New Delhi

Shugaba Mohamadou Issoufou, na Jamhuriyar Nijar a lokacin da karamin minista mai kula da manyan masana'antu na Indiya, G.M. Siddeshwara, yake tarbarsa.

Shugaba Idris Deby Ito na kasar Chadi a lokacin da ya isa zauren taron kolin Indiya da kasashen Afirka.

Shugaba Boni Yayi na Jamhuriyar Benin

Sakatare mai kula da yankunan yamma na Indiya, Navtej Singh Sarna, na biyu a dama, yana magana da wani wakilin Masar a ranar farko ta taron kolin Indiya da Kasashen Afirka a New Delhi

Shugaba John Dramani Mahama, na Ghana tare da maidakinsa, Lordina, a lokacin da karamin ministan Noma na Indiya, Mohanbhai Kundariya ke tarbarsu.

Karamin minista a gwamnatin Indiya, G M Siddeswara yana tarbar shugaba Ellen Johnson Sirleaf, ta kasar Liberiya.

Mataimakin shugaban kasar Tanzaniya, Mohammed Gharib Billal, a hagu, yana gaisawa da karamin ministan man fetur na Indiya, Dharmendra Pradhan, lokacin da ya isa wurin taron kolin.

Wani karamin minista a gwamnatin Indiya, Rajyavardhan Singh Rathore, yana tarbar shugaba Robert Mugabe na kasar Zimbabwe a lokacin da ya isa wurin taron kolin.

Karamin ministan al'adu na Indiya, Mahesh Sharma, yana tarbar firayim ministan kasar Lesotho, Pakalitha Mosisili.

Shugaba Ismail Omar Guelleh, na Djibouti, hagu, yana gaisawa da mai tarbarsa, karamin ministan harkokin wajen Indiya, Vijay Kumar Singh,lokacin da ya isa wurin taro

Bakin dake halartar taron kolin na Indiya da kasashen Afirka a New Delhi

Shugaba Yoweri Museveni na Uganda

Bakin dake halartar taron kolin na Indiya da kasashen Afirka a New Delhi