Shirin SURE-P Ya Gamu Da Cikas A Jihar Naija

Matasa Yan Kasuwa

wadansu matasa dake cin moriyar shirin nan na tallafin man fetir watau SURE-P da yawansu ya kai dubu daya da dari biyar sun shiga garari a cikin jihar Naija sakamakon gaza biyansu albashi na tsawon watanni bakwai.

A yanzu haka dai wadansu matasa dake cin moriyar shirin nan na tallafin man fetir watau SURE-P da yawansu ya kai dubu daya da dari biyar sun shiga garari a cikin jihar Naija.

Matasan sun bayyana cewa, basu san makomarsu ba, kasancewa sun shafe watanni bakwai ba a biyasu albashi ba, duk kuwa da cewa suna gudanar da aikin da aka sanya su karkashin shirin na SURE-P. Tsohuwar gwamnatin da ta gabata ce ta dauki matasan aiki, inda suke gudanar da ayyuka dabam dabam da suka hada da aikin duba gari, da kuma kula da cunkoson ababan hawa a kan titi, da kula da gandun daji. Sai dai matasan sun ce yanzu an barsu suna garari hannu wofi.

Shugaban tawagar matasan, Isa Abubakar Vatsa, ya bayyanawa wakilinmu Mustapha Nasiru Batsari cewa, a kowanne wata kamata ya yi a rika basu dubu goma sha biyar kowannensu. Yace an dakatar da biyansu tun daga watan OKtoba bara. Yace sun zauna da shugabannin shirin har sau biyar amma babu wani ci gaba da aka samu banda alkawura da ake masu da ba a cikawa.

Yace akwai marayu dake karkashinsu da suke wahala.

Sabuwar gwamnatin jihar tace, duk da yake ta san da matsalar, babu wani abinda zata iya yi sabili da karancin kudi da jihar ke fama da shi. Tace za a biya matasan da zarar an sami kudi daga gwamnatin tarayya kasancewa, shirin na gwamnatin tarayya ne.

Ga cikakken rahoton:

Your browser doesn’t support HTML5

Rahoton SURE-P-3:07