Wasan Matan Najeriya Da Amurka Shine Na Uku A Tarihi Wajen Yawan 'Yan Kallo

Kididdiga ta nuna cewa wasan kwallon kafa da aka yi a tsakanin Najeriya da Amurka a gasar cin kofin kwallon kafar mata ta duniya da ake yi a kasar Canada, shine na uku a duk tarihi a yawan wadanda suka kale shi a rukunin kwallon kafar mata a nan Amurka.

Gidan telebijin na FOX wanda ya nuna wasan na Najeriya da Amurka, yace anyi abubuwan tarihi masu yawa a wannan wasa.

Da farko dai, mutane miliyan 5 suka kamo tashar telebijin ta FOX don ganin wannan wasa. Kuma wannan wasa, shine na daya a duk tarihi a yawan wadanda suka kalli wani wasan zagayen farko na mata na duniya. Haka kuma, gidan telebijin na FOX bai taba nuna wasan da ya samu ‘yan kallo a tasharsa kamar wannan ba.

Wasan na matan Najeriya da Amurka, shine na uku a duk tarihi wajen yawan ‘yan nkallo a telebijin. Wasanni biyun da suka zarce shi kawai sune wasan karshe na cin kofin mata na duniya tsakanin Amurka da China a 1999, da kuma wasan karshe na cin kofin mata na duniya tsakanin Amurka da Japan a 2011. Wasan da yake matsayin na uku, a yanzu kuma ya ja baya zuwa na hudu, shine wasan kusa da karshe a gasar cin kofin mata ta duniya ta 1999 a tsakanin Amurka da Brazil.