A wani matakin da yayi kama da abubuwan da suka faru a majalisar wakilan Najeriya a 2011, 'yan jam'iyyar APC masu goyon bayan Bukola Saraki sun hada kai da 'yan jam'iyyar adawa ta PDP suka zabi tsohon gwamnan na jihar Kwara a zaman sabon shugaban majalisar dattijai.
Haka kuma, an zabi dan jam'iyyar PDP mai adawa, Ike Ekweremadu, a matsayin mataimakin shugaban majalisar, ya kayar da sanata Ali Ndume na jam'iyyar APC a wannan zaben da mafi yawan 'ya'yan jam'iyyar APC ba su cikin zauren a lokacin da aka gudanar da shi.
Sanatoci 57 kawai suka halarci zaben shugabannin, yayi9n da wasu sanatoci 51, akasarinsu 'ya'yan jam'iyyar APOC, suke can dakin taro na kasa da kasa inda suka ce an tura su domin ganawa da shugaba Muhammadu Buhari.
Wakiliyarmu Madina Dauda, ta ce yanzu haka dai ana can ana kokarin yin zabe a majalisar wakilai.