Ana Kwashe Wadanda Suka Jikkata Daga Tashin Bam Daren Nan A Gombe

Wani bangaren ofishin ‘yan sanda da aka kaiwa hari a Gombe a shekarar 2011

Ana ci gaba da kwashe gawarwakin wadanda suka mutu tare da mkutanen da suka ji rauni a sanadin tashin wani bam cikin daren nan na Jumma'a a dab da kasuwar mata dake unguwar Arawa a garin Gombe.

Bam ya tashi dab da lookacin sallar Isha, amma ya zuwa yanzu babu cikakken bayani a kan ko an dasa bam din ne aka bar shi a wurin, ko harin kunar bakin wake ne, ko kuma dai ya tashi ne bisa kuskure.

Mun tattauna da wani dan unguwar Herwa Gana a Gombe, Garba Tela, wanda dan siyasa ne, da kuma wakilinmu na yankin, Abdulwahab Muhammad, wadanda suka yi mana cikakken bayani a www.dandalinvoa.com na abubuwan da suka faru kuma suke faruwa.

Idan ba a manta ba, a yau din da asuba ne 'yan sanda a Gombe suka kama wata mota dauke da bama-bamai har guda 5 a cikinta. Shin ko akwai alaka a tsakanin wadannan abubuwa biyu?

A saurari bayani.....

Your browser doesn’t support HTML5

Bayanin Halin Da Ake Ciki A Gombe Bayan Tashin Bam A Kasuwar Arawa - 11'26