Abubuwa 10 Da Suka Girgiza Duniyar Kwallo A 2014: A Kan Nawa FC Barcelona Ta Sayi Neymar?

Shugaban FC barcelona na lokacin, Sandro Rosell yana maraba da Neymar lokacin da kulob din ta saye shi.

A lamba ta 4 daga cikin abubuwa guda 10 da editocin GOAL.COM suka bayyana a zaman wadanda suka fi girgiza duniyar kwallon kafa a shekarar 2014, abin fallasar nan da ta shafi sayen dan wasa Neymar da kungiyar FC Barcelona ta yi.

Wannan abin fallasa daga karshe ta kai ga murabus din shugaban kungiyar, Sandro Rossell, wanda da farko yace ai sun sayi Neymar a kan kudi Euro miliyan 57 ne, har ma yana shagube ma abokiyar adawarsu Real Madrid a kan ta sayi Gareth Bale kan kudi fiye da Euro miliyan 90.

Daga baya, sai bincike ya nuna cewa ashe dai FC Barcelona ta sayi Neymar ne a kan kudi fiye da Euro miliyan 95, kuma sai aka gano cewa ashe ma fiye da rabin wannan kudin, an biya shi ne ga mahaifin Neymar, wanda shi ma sunansa Neymar babba, wanda shi ne manajan dan nasa.

Tun da aka fara kwallon kafa a duniya, babu wani manajan dan wasa da ya taba samun kudin kamasho irin wannan, a duk duniya, watau kashi 70 cikin 100 na kudin da aka biya dan wasa.

Muna tafe da matsayin gantsara cizon da Luis Suarez yayi ma dan wasan Italiya, da kuma dukar kawo wuka na 7-1 da Jamus ta yi ma Brazil duk a lokacin gasar cin kofin duniya.