Abubbuwa 10 Da Suka Girgiza Duniyar Kwallon Kafa A 2014: Lamba Ta 6

'Yan wasan Atletico Madrid su na jefa kwach nasu, Diego Simeone, sama don murnar lashe kofin La Liga da suka yi, Asabar 17 Mayu, 2014

A lamba ta 6 cikin jerin abubuwa 10 da suka girgiza duniyar kwallon kafa a shekarar 2014, shi ne lashe kofin wasannin lig-lig na kasar Spain da kungiyar Atletico Madrid ta yi.

Babu wanda ya taba tunanin cewa yaran na Diego Simeone zasu iya cimma wannan tazara, amma a wasansu na karshe, sun dage suka yi kunnen doki da kungiyar FC Barcelona, suka ci gaba da rike matsayi na daya, suka kuma damke kofin La Liga a gaban babbar abokiyar adawarsu, ita ma ta birnin Madrid, watau Real Madrid.

Wannan abinda Atletico Madrid ta yi, ya kawo karshen shekaru 10 da aka shafe a kasar inda sai kungiyoyi kwaya biyu rak suke lashe wannan kofi na La Liga, watau Real Madrid da FC Barcelona.

A lamba ta 5 da zamu duba a shirinmu na gaba, nahiyar Afirka zamu dosa, kamar dai yadda editocin GOAL.COM suka zayyana wadannan abubuwa 10 da suka ce sune suka fi tasiri wajen girgiza duniyar kwallon kafa a shekarar 2014.