Wani dan kunar-bakin-wake da yayi niyyar hallaka jama'a a garin Gombe yau alhamis da safe, ya hallaka kansa shi kadai, wasu dake kusa da nan kuma suka ji rauni.
Wannan shi ne karo na uku da 'yan kunar-bakin wake ke aniyar kai hari a garin Gombe tsakanin jiya da yau, amma a duk lokutan, sune ke hallaka kawunansu.
Kakakin 'yan sandan jihar Gombe, DSP Fwaji Attajiri, yace wannan dan kunar bakin wake yazo shi a kan babur, inda yayi niyyar shiga wani wurin da majami'a ta ke, amma aka hana shi.
Ana cikin wannan ne sai bam din da ya boye a jikinsa ya tashi, ya hallaka shi.
A jiya ma, an yi niyyar kai harin kunar bakin wake a barikin sojojin garin na Gombe, amma sai dan kunar bakin waken kawai ta mutu. A cikin dare ma an sake jin karar tashin wani bam din a ta wajejen barikin sojan.
Ga cikakken rahoto...
Your browser doesn’t support HTML5