WASHINGTON, DC —
Hare-haren ‘yan Boko Haram, ya tilastawa kamfanin samar da wutar lantarki, dake kula da jihohin Adamawa, Borno, Yobe da kuma Taraba rufe wasu ofisoshin kamfanin, a arewa maso gabashin Najeriya.
Hakkan ya jawo matsalar wutar lantarki, a wadannan jihohi, da yake karin haske dagane da wannan batu, jami’in hurda da jama’a, na kamfanin Alhaji Aliyu Hassan Ardo, yace kamfanin a yanzu, yana fama da karanci kudaden shiga.
Bayan matsalar samar da wutar lantarki, hare-haren na Boko Haram ya durkusarda harkokin kasuwancin a wadannan jihohi, inda a bangare guda hedkwatar tsaron Najeriya ta rufe wasu iyakokin kasar da kasar Kamaru, wanda a baya kuwa akan samu hada-hadan kasuwanci tsakanin al-umar kasacen biyu.