A lamba ta 7 cikin jerin abubuwa 10 da suka girgiza duniyar kwallon kafa a shekarar 2014, yadda ‘yar mitsitsiyar kasar nan da ake kira Tsibiran Faroe, ta doke kasar Gireka ko Greece da ci 1 da babu a wasan share fagen shiga gasar Turai ta 2016.
A lokacin da aka buga wannan wasa a watan Nuwambar 2014, kasar Girka it ace ta 18 a duniya, yayin da Faroe Island take ta 187. Kuma kafin wannan karawa, kasar Girka tana doke Faroe Islands da ci 5 a duk karawar da suka taba yi. Wannan karon, reshe ya juye da mujiya, har wasu masana kwallo suka ce wannan sakamako, kamar a ce tsibirin Monserrat ce ta doke Jamus a kwallo, ko kuma a ce Brazil ta sha kasha a hannun tsibirin Sao Tome.
Wannan nasara da Faroe Island ta samu a kan Girka ta haddasa kawo karshen mulkin Claudio Ranieri, tsohon manajan Chelsea, wanda ya gaji Fernando Santos a matsayin kwach na kasar Girka a bayan gasar cin kofin kwallon kafar duniya ta 2014 a Brazil.
Gobe zamu ji wasa na 6 da ya girgiza duniyar kwallon kafa a 2014.