Maidakina Ta Hana ni Karbar Mukamin Kwach na Ingila In Ji Jose Mourinho

Manajan Chelsea, José Mourinho

Jose Mourinho yace matarsa Matilde Faria, itace ta lallabashi domin karya karbi matsayin manaja na kungiyar kwallon kafar Ingila a shekara ta 2007.

A lokacin, Mourinho, wanda ke rike da matsayin manaja na kungiyar Chelsea a yanzu haka, ya so ya zamo magajin Steve McClaren a matsayin kwach na kasar Ingila. Amma yace hirar da sukayi da matarsa itace ta sashi yin tunanin yadda ba zai ji dadin rayuwa ba a tsakanin wasa da wasa, tunda a kan dauki watanni masu yawa kafin kasa ta buga wani wasa guda.

Yace, tayi gaskiya, kuma lokaci bai yin a karbar wannan matsayin ba. Yace, “ina matukar son aikin manajan kulob wanda shi a kullum ake yinsa, ina kuma son matsin lamba da aikin ke kawowa a kullum, wasannin horo, tafiye-tafiye zuwa buga wasanni, harma da karawar gasannin wasanni.

Mourinho yace, a lokacin da yake tunanin karbar mukamin manajan Ingila, kasar tana shirin buga wasan sada zumunci da Faransa a Paris ne, don haka har ya fara tunanin ‘yan wasan da zai gayyata da irin dabarar kwallon da zasu buga. A nan ne sai matarsa tazo ta ce masa yaushe ne wasan Ingila na gaba? Sai yace mata nan da wata biyu. Ta ce masa me zaka yi cikin watanni biyu kafin wasan? Shi kansa sai ya ji cewa a gaskiya ba zai iya ba, watakila sai nan da shekara 20.

Your browser doesn’t support HTML5

Jose Mourinho - 1'19"