Kungiyar kwallon kafa ta FC Barcelona ta samu nasarar daukaka karar da ta yi a game da katin jan kunne, ko yellow card, da aka ba dan wasanta Lionel Messi, a bayan da wani dan kallo ya jefe shi da kwalba a wasan da suka yi da Valencia a karshen makon da ya shige.
An jefi Messi da kwalba a lokacin da shi da sauran ‘yan wasan Barcelona suke murnar kwallon da Sergio Busquet ya jefa musu ana dab da tashi daga wasa suka yi nasara da ci daya da babu.
Daga nan ne Messi yaje ya kai kuka ga alkalin wasa, Fernandez Borbalan cewa an jefe shi, amma sai alkalin wasan yaba shi katin gargadin bisa hujjar cewa Messi yana jinkirta komawa cikin filin wasan ne domin ya cinye lokaci har a hura tashi.
Kungiyar Valencia dai ta ce zata zakulo dan kallon da ya jefi Messi kuma in ta gano shi har abada ba zai sake shiga wani was anta ba.
Hukumar kwallon kafa ta Spain a yanzu ta ce zata cire wannan katin jan kunne daga cikin fayil na Lionel Messi a bayan nasarar daukaka karar da FC Barcelona ta yi.