Har Yanzu Da Sauran Mai A Tankin Didier Drogba In Ji Mourinho

Didier Drogba na Chelsea a karawarsu da Bayern Munich a gasar cin kofin zakarun kulob na Turai

A bayan wasan da Chelsea ta yi da Tottenham jiya laraba da daddare, manajan Chelsea, Jose Mourinho, ya bude ya tambayi ‘yan jaridar dake masa tambayoyi wai shin sun tuno Diego Costa kuwa a yau? Ya amsa ma kansa da cewa, shi kam bai tuno da shi ba.

Da yawa sun yi mamaki da yake cewa Costa shi ne dan wasan gaba mafi kwarjini na Chelsea, kuma shi ne ya fi jefa mata kwallo a ragar abokan karawa. Sannan shi ne na biyu a duk Firimiya Lig wajen yawan kwallaye, inda ya jefa 11 a kakar bana.

Amma kuma, Mourinho yayi haka ne domin nuna imanin da yayi kan dadadden dan wasa Didier Drogba, mai shekaru 36 da haihuwa, wanda ya jefa kwallo guda, ya kuma bayar da guda aka jefa a wasan 3 da 1 da Chelsea ta yi ma Tottenham.

Koda yake Drogba ba zai iya buga wasa sau 2 a sati kamar yadda yake yi a da ba, kuma koda yake bay a da sauri da kuzari kamar da, har yanzu, tamaula ba ta bar shi ba, kuma zai iya bugawa a kowane fage na tamaula.

Mourinho yace, "Drogba mutum ne dabam. Na farko dai bay a son kai, ba ya da girman kai. Yana wasa ne ma kungiyarsa. Ko an fara wasa da shi, ko kuma an sanya shi daga baya ne domin maye gurbin wani, haka yake wasansa da kuzari."

Your browser doesn’t support HTML5

Har yanzu Da Sauran Drogba In Ji Mourinho - 1'10"