Dan wasan FC Barcelona, Lionel Messi, ya sake yin wani abin tarihin a fagen tamaula, kwanaki kadan bayan da ya kafa wani abin tarihin kuma.
Jiya talata, Messi ya jefa kwallaye har uku a ragar APOEL, ya zarce tsohon dan wasan Real Madrid, Raul, a zaman wanda ya fi jefa kwallaye cikin raga a gasar zakarun kulob kulob na Turai.
A bayan da Luis Suarez ya jefa kwallon farko a wasan na jiya talata, Messi ya bi bayansa da kwallaye har uku. A ranar asabar ma, Messi ya jefa kwallaye har uku a karawar FC Barcelona da Sevilla, ya zamo dan wasan da ya fi jefa kwallaye a ragar a wasannin lig-lig na kasar Spain, La Liga.
Yanzu Messi yana da kwallaye 74 a gasar cin kofin zakarun kulob-kulob na Turai, watau kwallaye uku fiye da Raul.
A wata mai zuwa FC Barcelona zata yi kokarin zamowa ta daya a saman rukunin F na gasar cin kofin zakarun kulob kulob na Turai a karawar da zata yi da zakarun lig na Faransa, PSG.
Messi yace PSG ba kanwar lasa b ace, amma zasu yi kokarin doke su.