WASHINGTON, DC —
Jama’a assalamu alaikum. Majalisar dattijan Najeriya ta yi watsi da batun kara wa’adin aiki da dokar ta baci a jihohin arewacin Najeriya, haka kuma ta titsiye manyan hafsoshin sojan kasar na tsawon sa’o’I 7 tana musu tambayoyi. Sanata Kabiru Gaya yace basu gamsu da amsoshin da suka ji ba.
Shi ma Alkali Abdulkadir Jajere, yace dokar ta baci dai ta riga ta tafi, kuma su kansu sojojin sun yarda cewa an bas u duk abinda suka nema na shawo kan Boko Haram.
Sanata Kabiru Marafa, yace batun saka sojoji a kan tituna sun a gallazawa jama’a yayin da ‘yan ta’adda ke cin karensu babu babbaka, na daya daga cikin abubuwan da suka tado da su a tattaunawar tasu.
Ga cikakken rahoton nan...
Your browser doesn’t support HTML5