Idan har kana farauta, ko gyarawa ko kuma cin naman daji, tilas kayi hattara.
Wasu dabbobi kamar jemagu, birai da goggo suna dauke da kwayar cutar dake janyo Ebola.
Ebola ba cutar fararen fata ba ce, ba wai masu aikin agaji na jinkai ne suka kawo ta kasashenmu ba.
An fara gano kwayar cutar a shekarar 1976, aka kuma sanya mata sunan inda aka fara ganinta a kogin Ebola dake kasar Kwango Kinshasa.
Masana kimiyya sun yi imanin cewa jemagu sune ke dauke da wannan kwayar cuta tun asali.
An yi imanin cewa kwayar cutar ta fara shiga jikin dan Adama ta hanyar tabawa ko cin naman daji.
Masu farauta a cikin daji su na fuskantar hatsari na zahiri. Kwarzani ko cizo ko yanka daga wata dabbar dake dauke da kwayar cutar nan tana iya sanya shi jikin mutum. Haka kuma gyaran naman dabbar daji maras lafiya na iya sanyawa mutum cutar.
Cin naman daji hanyar rayuwa ce a tsakanin al’ummomi da yawa namu. Amma kuma tilas mu gujewa naman daji muddin dai akwai yiwuwar kamuwa da cutar Ebola.
Nazarci gaskiyar cutar Ebola. Hakan na iya ceton ranka.
Your browser doesn’t support HTML5