Cutar Ebola ba jifa ce ko wani abin tsibbu ba, cut ace mai kisa ta zazzabin da ake kamawa daga taba ruwan jikin wanda ke dauke da cutar.
Alamunta su kan fara daga zazzabi, kasala da kuma ciwon jijiyoyin jiki. A bayan ‘yan kwanaki kadan, sai a fara amai da zawayi, inda jikin mutum yake zubar da lita 4 na ruwan jiki a kullum.
Ebola tana da saurin yaduwa. Idan mutum ya ga irin wadannan alamun a jikinsa, to ya gaggauta zuwa asibiti.
Tilas mutum yak are kansa ta hanyar wanke hannu a kai a kai. Kada mutum ya ci, ko kuma ya taba naman daji. A guji kusantar wadanda suka kamu da cutar Ebola. Haka kuma, kada a taba gawar wadanda cutar Ebola ta kasha.
Idan har mutum yayi cudanya da wanda ke fama da cutar Ebola, , tilas ya rika auna zafin jikinsa a kullum ko zai ga wani sauyi. Ganowa da jinyar Ebola da sauri yana da matukar muhimmanci wajen rayuwa.
Nazarci gaskiyar cutar Ebola. Hakan na iya ceton ranka.